- ABNA 24 - ya habarta maku cewa: an gudanar da maulidin Amirul Muminin (a.s.) a Husainiyar Imam Ali (a.s.) a birnin Saint Petersburg na kasar Rasha. Hujjatul-Islam Wal-Muslimeen "Muhammed Ali Muinian" mataimakin shugaban harkokin kasa da kasa na Majalisar Ahlul-Baiti (AS) Ta Duniya ya halarci wannan taron inda ya gabatar da jawabi ga mahalarta taron tare da gabatar da kyautar banar Ahlulbaiti ta wannan majalisa zuwa ga Husainiyyar Imam Ali (A.S.).